Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Fulani Da Matasa Na Kiran A Ba Da Hadin Kai Ma Buhari


Wasu matasan Fulani
Wasu matasan Fulani

Yayin da ake cigaba da tsokaci kan irin gwamnatin da Shugaban Najeriya mai barin gado Janar Muhammadu Buhari zai kafa, kungiyoyin Fulani da na matasa na kirfan 'yan Najeriya su ba shi hadin kai da kuma lokaci.

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyatti Allah ta bayyana farin cikinta na nasarar da Janar Muhammadu Buhari (murabus) ya yi. Babban Sakataren Kungiyar Miyatti Allah na kasa Malam Baba Usaman Galdama, wanda ya bayyana hakan, ya kuma yi kira ga ‘yan kungiyar da a ba janar Buhari goyon baya, ya kuma ce Buhari adali ne, kuma hakan ya sa aka zabe shi. Ya ce sun tabbatar cewa Buhari zai dau matakin da ya dace don kasa ta zauna lafiya don haka lallai ‘yan kungiyar ta Miyatti Allah su ba shi lokaci da kuma goyon baya saboda babu wanda ya san matsalolin kungiyar kamar Buhari.

Malam Galdama ya ce muddun Janar Buhari ya magance matsalar tsaro to duk sauran gyare-gyara za su biyo baya. Ya ce lallai ya kamata a ba gwamnatin Buhari mai zuwa lokaci ganin irin dinbin barnar da aka yi a kasar, wadda gyararta sai a hankali.

To baya ga Fulanin, ita ma hadakar kungiyar matasan arewacin Najeriya ta yi irin wannan jan hankalin ga mambobinta game da abubuwan da su ke sa ran Buhari zai cimma. Shugaban hadakar kungiyoyin matasan arewan, Hassan Waziri Cinade, y ace ya kamata matasan arewa su gode ma Allah saboda canjin da aka samu. To amma y ace dole ne a saurara ma Buhari ganin girmar matsalar da zai gada, a cewar wakilinmu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG