An hallaka a kalla mutane biyu a yayin da wasu kuma da dama su ka sami raunuka a babban birnin janhuriyar dimokaradiyyar Congo a rana ta karshe ta yakin neman zabe na zaben da za a gudanar a gobe Litini.
‘Yan sanda a birnin Kinshasa sun hana gangamin siyasa a jiya Asabar bayan da mogoya bayan shugaba mai ci Joseph Kabila su ka fafata da magoya bayan babban mai kalubalantarsa Etiene Tshisekedi.
Shugaba Kabila ya soke nesa gangamin, to amman sai Mr. Tshisekedi ya nace sai ya yi watsi da umurnin hana gangamin ya gudanar da nasa a dandalin wasannin motsa jiki mafi girma a Kinshasa. Dubban mutane ne su ka hallara a filin jirgin saman Kinshasa don marabtarsa, to amman sai ‘yan sanda su ka hana tawagarsa fita daga jirgin saman.
Jami’an tsaro sun yi amfani da barkwonon tsohuwa da ruwan zafi don tarwatsa taron jama’ar. Shaidu sun ce an yi ta harbe-harbe kuma sun ga gawarwaki.
A wurare da daman a yakin neman zabe, mogoya bayan mutanen biyu sun yi ta fafatawa.