Wata jam’iyyar siyasa mai bin tafarkin Islama mai sassauci ta ci yawancin kujerun Majalisar tarayyar Morokko kuma it ace za ta jagoranci kafa sabuwar gwamnati a kasar.
Gwamnati ta fadi jiya Asabar cewa sakamakon wuccin gadi na zaben da aka gudanar ranar Jumma’a ya nuna cewa jam’iyyar Justice and Development Party (PJD a takaice) ta ci kashi daya cikin biyar na kujerun Majalisar mai jimlar kujeru 395.
Jam’iyyar su Farayim Minsta Abbas el Fassi ta Nationalist Istiqal Party ce ta zo ta biyu. Kamfanin dillancin labaran Reuters y ace Firayim Minstan ya bayyana nasarar ta PJD da cewa nasara ce ta dimokaradiyya.