‘Yan sandan kwantar da tarzoman Misra sun yi ta harba barkonon tsohuwa da harsasan roba sannan su ka abka cikin dandalin Tahrir na birni al-Khahira da safiyar jiya Asabar don su wargaza tantunan da masu zanga-zanga su ka kafa tun ran Jumma’a, su ka kashe mutum guda suka kuma raunata wasu fiye da 650.
Shaidu sun ce rigimar ta barke ne bayan da ‘yan sanda su ka tutture tantunan masu zanga-zanga kimanin su 100, wadanda su ka taru a dandalin tun da dare a wani yinkuri na sake zanga-zangar mamaye dandalin na lokaci mai tsawo, bayan wata babbar zanga-zangar da aka yin a kyamar manufofin gwamnatin mulkin sojin kasar ranar Jumma’a.
Dinbin jama’a sun abka wa wata motar yaki, suka banka mata wuta suna ta jifan ‘yan sanda da duwatsu.
Wannan boren ya yana tuni da zanga-zangar kyamar gwamnatin da ta kai ga kawo karshen shugabancin tsohon shugaba Hosni Mubarak a cikin watan Fabrairu.
Wannan tashin hankalin ya janyo fargabar yiwuwar sabon yamutsi kafin zaben farko na Majalisar Dokokin Misra tun bayan hanbarar da Mr. Mubarak. An tsai da wani lokaci a karshen wannan wata don gudanar da zaben.
Masu zanga-zangar da su ka kai dubbai a dandalin ranar Jumma’a, suna nuna bacin ransu ne kan wata kwaskwarimar da gwamnati ke son yi a kundin tsarin mulki, wanda masu sukar shirin ke cewa wata dabara ce ta tsawanta mulkin wuccin gadin na soji.