Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbe Mutane Da Dama A Wata Zanga-zangar Adawa Da Karin Kudin Haraji A Kenya


Zanga-zangar Adawa Ta Kin Karin Kudin Haraji Da Tsadar Kayan Masarufi A Kenya, Mutane Sun Kona Motoci Da Tayoyi
Zanga-zangar Adawa Ta Kin Karin Kudin Haraji Da Tsadar Kayan Masarufi A Kenya, Mutane Sun Kona Motoci Da Tayoyi

An harbe mutane da dama a Kenya, da ake kyautata zaton wadansu sun rasa rayukansu, yayin da jami'an tsaro suka yi arangama da masu zanga-zanga a fadin kasar domin nuna adawa da tsadar rayuwa da karin haraji, in ji wani jami'in asibiti da kafafen yada labarai na kasar a jiya Laraba.

WASHINGTON, D.C - Masu zanga-zangar dai sun yi ta jifan 'yan sanda da duwatsu tare da kona tayoyi a kan tituna, yayin da jami'an tsaro su kuma suka harba hayaki mai sa hawaye, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Masu Zanga-zangar Adawa A Kenya Ta Kin Karin Kudin Haraji Da Tsadar Kayan Masarufi A Kasar
Masu Zanga-zangar Adawa A Kenya Ta Kin Karin Kudin Haraji Da Tsadar Kayan Masarufi A Kasar

Wannan dai shi ne zagaye na uku na zanga-zangar adawa na masu kin gwamnati da 'yan adawa suka kira a wannan watan.

'Yan sanda sun kama akalla mutane 300 a fadin kasar, ciki har da manyan 'yan adawa tara, a cewar ma'aikatar cikin gida da kuma lauyan 'yan adawa.

‘Yan Sanda Sun Yi Feshin Hayaki Mai Barkono Akan Masu Zanga-zangar Adawa A Kenya
‘Yan Sanda Sun Yi Feshin Hayaki Mai Barkono Akan Masu Zanga-zangar Adawa A Kenya

Hakan ya sa aka kai ga rufe makarantu a Nairobi babban birnin kasar, birnin Mombasa mai tashar jiragen ruwa da Kisumu, birni na uku mafi girma a kasar. Babban birnin na Nairobi ya kasance babu kowa, duk an watse, inda aka rufe kasuwanni da dama, yayin da 'yan sanda suka kafa shingayen binciken ababen hawa a kan hanyoyin da ke zuwa fadar shugaban kasa, na William Ruto.

An zabi Shugaba Ruto ne dai a watan Agustan da ya gabata, inda ya yi alkawarin kare muradun talakawa, to amma farashin kayayyakin masarufi ya tashi a karkashin gwamnatinsa kuma a watan da ya gabata gwamnatinsa ta zartas da karin haraji.

Zanga-zangar Adawa A Kenya
Zanga-zangar Adawa A Kenya

Gwamnati ta ce ana bukatar haraji ne kan man fetur da gidaje don taimakawa wajen magance karuwar biyan basussuka da kuma samar da hanyoyin samar da ayyukan yi.

Wani mai zanga-zangar a birnin Mombasa wanda ya bayyana sunansa da Eric kawai, Eric, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a lokacin da yake zuba ruwa a fuskarsa domin ya wanke hayaki mai sa hawaye cewa, "Wannan gwamnati tana taka dokar kundin tsarin mulkin kasar ne ta hanyar zaluntar mu yayin da muke kokarin tabbatar da tsarin mulki daya ta hanyar zanga-zangar lumana.”

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG