Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Afirka

Shugaban Adawa a Kenya Ya Yi Kira Ga 'Yan Kasar Su Fito Zanga-Zanga


Kenya Opposition Protests
Kenya Opposition Protests

Shugaban adawa na kasar Kenya Raila Odinga ya yi kira ga al'ummar kasar su fita su gudanar zanga zangar kin jinin gwamnati bisa tsadar rayuwa.

Yau Litinin, Birnin Nairobi da sauran birane a Kenya suna shirin tukarar zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa karkashin mulkin shugaba William Ruto.

‘Yan sanda sun haramta zanga-zangar a ranar Lahadi sai dai kuma Odinga ya karfafawa ‘yan Kenya gwiwa su hallarci zanga-zangar.

An kashe mutum daya a Nairobi babban birnin Kenya yau Litinin sannan an raunata ‘yan sanda da dama a wata arangamar da suka yi da masu zanga-zangar.

Zanga-Zanga a Kenya
Zanga-Zanga a Kenya

Hukumar layin dogon Kenya ta fitar da wata sanarwa a ranar Lahadi dake cewa "an soke dukkanin zurga-zurgar layin dogo na gobe a sakamakon wasu al’amura da baza a iya kauce musu ba". Odinga ya bukaci ‘yan Kenya su fito kan tituna a yau Litini da ranar Lahadi domin yin zanga-zanga.

XS
SM
MD
LG