Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Harba Barkonan Tsohuwa Akan Masu Zanga-zanga A Kenya 

'Yan Sanda Sun Harba Barkonan Tsohuwa Akan Masu Zanga-zanga A Kenya
'Yan Sanda Sun Harba Barkonan Tsohuwa Akan Masu Zanga-zanga A Kenya

‘Yan sandan Kenya sun harba barkonon tsohuwa kan daruruwan mutanen da ke zanga-zanga a kusa da majalisar dokoki a birnin Nairobi a ranar Talata, 6 ga watan Yuni.

WASHINGTON, D.C. - Jama’a na zanga zangar ne don nuna adawa da kudirin doka da za ta shafi hadahadar kudade wacce za ta kara haraji kan man fetur da gidaje.

'Yan Sanda Sun Harba Barkonan Tsohuwa Akan Masu Zanga-zanga A Kenya
'Yan Sanda Sun Harba Barkonan Tsohuwa Akan Masu Zanga-zanga A Kenya

Shugaban kasar William Ruto, wanda ya lashe zabe a watan Agusta da kamfen din taimakawa talakawa, yana fuskantar matsin lamba na ya tara kudaden shiga a bangaren tattalin arziki, sakamakon karuwar biyan basussukan da gwamnati ke yi.

Sai dai shawarwarin nasa sun sha suka daga ma'aikatan gwamnati da 'yan adawar siyasa, wadanda ke cewa tsadar rayuwa ta yi muni.

'Yan sanda sun ta harba barkonon tsohuwa ne domin tarwatsa masu zanga-zanga kimanin 500 da suka yi tattaki zuwa majalisar dokokin kasar domin gabatar da koke na adawa kan kudirin, kamar yadda wani shaida ya fadawa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.

'Yan Sanda Sun Harba Barkonan Tsohuwa Akan Masu Zanga-zanga A Kenya
'Yan Sanda Sun Harba Barkonan Tsohuwa Akan Masu Zanga-zanga A Kenya

Shugaba Ruto ya kare kudirin, yana mai cewa ana bukatar tanade-tanade ne domin karin tattalin arziki da tanadin kudi na samun ayyukan yi ga matasa ta hanyar gina sabbin gidaje da ake samun kudaden shiga ta hanyar harajin gidaje.

Ana sa ran za a kada kuri'a kan dokar, wacce kuma za ta kara haraji kan ayyukan dijital a mako mai zuwa.

Jam'iyyar adawa ta Azimio La Umoja (Declaration of Unity) wacce tun a watan Maris ta jagoranci zanga-zangar adawa da gwamnati kan tsadar rayuwa da kuma magudin zabe da aka yi a zaben bara, ta ce wannan kudirin dokar zai mayar da kasar zuwa kamar shekarun 1980, lokacin da tattalin arzikin kasar ya fara lalacewa.

'Yan Sanda Sun Harba Barkonan Tsohuwa Akan Masu Zanga-zanga A Kenya
'Yan Sanda Sun Harba Barkonan Tsohuwa Akan Masu Zanga-zanga A Kenya

A makon da ya gabata ne 'yan adawa suka dakatar da tattaunawar da ake yi a majalisar dokokin kasar da nufin kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsu da gwamnati. Shugabansu Raila Odinga dama ya yi barazanar sake gudanar da zanga-zangar.

Kungiyoyin kwadago da suka hada da daya da ke wakiltar ma’aikatan lafiya, su ma sun yi zanga-zangar nuna adawa da kudirin dokar a makon jiya.

-Reuters

XS
SM
MD
LG