Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MAIDUGURI: Kungiyar Boko Haram ta Kai Hari


Wurin da dan kunar bakin wake ya tayar da bam a Maiduguri
Wurin da dan kunar bakin wake ya tayar da bam a Maiduguri

Yau da safe wani bom ya tashi a kasuwar titin Gamboru dake cikin Maiduguri jihar Borno

Wani dan keke napep ne ya tsaya tsakiyar hanya da keken kana ya tayar da bom a kan hanyar titin Gamboru kusa da kasuwar kwastan.

Bom din da ya tayar da misalin karfe bakwai na safe ya yi sanadiyar mutuwar mutane bakwai da shi dan kunar bakin waken da yasa adadin wadanda suka mutu ya kai takwas.

Banda wadanda suka mutu akwai wasu guda bakwai da suka jikata.

Shaidun gani da ido sun shaidawa Muryar Amurka wani dan kunar bakin wake ne da ya zo cikin keke-napep mai kafafuwa uku ya tsaya tsakiyar titi kafin ya tada bom din.

Tuni jami'an tsaro suka killace wurin. An kwashe gawar wadanda suka mutu wadanda kuma suka jikata an kaisu asibiti.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG