Kanar Tukur Gusau mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar soji ta bakwai dake Maiduguri ya tabbatar da kwato mutane 30 a cigaba da binciken da suke yi bayan sun fatattaki 'yan kungiyar Boko Haram.
Bayan sun sake cafke garin sojoji na bi gida gida da kwararo kwararo domin tabbatar cewa babu wani dan ta'ada kodaya da ya makale wani wuri da nufin yin cuta. Suna kuma binciken ko an boye bamabamai da wasu makamai.
A yayinda suke bincike ne suka samu mutane a yankuna biyu na Wufe da kuma Kwayafe. Sun samu mutane talatin da suka hada da yara 21 da suka hada da dan kwanaki shida da haihuwa yayin da sauran 'yan kasa da shekaru bakwai ne. Akwai mata guda bakwai cikinsu uku na jego. Akwai maza da suka manyanta guda biyu. Mutanen suna hannun sojoji suna kula dasu. Wasu cikin mutanen suna fama da raunuka daban daban.
Rundunar ta samu wani wuri a fadar Shehun Dikwa wanda 'yan Boko Haram suka kebe musamman suna koyas da aikin ta'adanci kamar su dabarun harba bindigogi da yadda za'a harbo jirgin sama.
A halin yanzu 'yan ta'adan sun lalata fadar ta yadda Shehun Dikwa baya iya zama ciki. Sun wawure duk kayan dake cikin fadar.
Inji Kanar Tukur Gusau mutanen da suka ceto sun galabaita. Yanayinsu nada ban tausayi. Duk jikinsu nada raunuka.
Kawo yanzu duk mutanen garin Dikwa sun fice babu kowa.
Ga karin bayani.