Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani mai harin kunar bakin wake ya kashe mutane takwas a Potiskum


Harin kunar bakin wake
Harin kunar bakin wake

Yau Lahadi wani mai harin kunar bakin wake ya kashe mutane takwas, a wata Majami'a a garin Potiskum, jihar Yobe arewa maso gabashin Nigeria.

Shugaba Mohammadu Buhari na Nigeria yayi kira ga Musulmi da su yiwa tarzomar kungiyar Boko Haram tofin Allah tsine.
Jiya Asabar shugaban yayi wannan kira bayan hare haren kunar bakin wake da ake ta kaiwa a jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria tun lokacinda aka fara azumi.
A daya daga cikin hare hare na baya bayan da aka kai, yan sanda sunce wata mace mai harin kunar bakin wake ce ta tarwatsa kanta cikin mutane da suke arcewa harin da kungiyar Boko Haram ta kai a kauyen Zabamari kusa da birnin Maiduguri.
Hukumomi sunce mutane da dama ne suka mutu a harin da aka kai Zabamari a daren Juma'a

A yayinda shugaban na Nigeria ke wannan bukata, sai kuma gashi a yau Lahadin nan wani mai harin kunar bakin wake ya kashe mutane takwas a wata Majami'a a garin Potiskum, jihar Yobe arewa maso gabashin Nigeria, kamar yadda wakilin sashen Hausa Haruna Dauda Biu ya aiko da rahoto.

Wani Mai Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane Takwas A Potiskum -
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG