Yau Asabar wani mai harin kunar bakin wake ya kai hari wata kasuwa a Ndjamena baban birnin kasar Chadi ya kashe mutane goma.
Kamfanin dilancin labaru Faransa ya bada labarin cewa mai harin kunar bakin waken yayi sigan burtu, ya sanya hijabi kamar mace.
Wannan al'amari ya faru ne sa'o'i bayan da aka kashe mutane goma a arewa maso gaashin Nigeria lokacinda 'yan Boko Haram suka kai hari wani kauye, suka kuma mamaye wata babar hanya a yankin.
Nan da nan babu wata kungiyar data yi ikirarin kai harin na Chadi daya raunana mutane da dama. To amma duk da haka hukumomi suna tsamanin kungiyar Boko Haram ce ta kai harin, wadda ta ke kai hare hare da dama a Nigeria.
Mai magana da yawun 'yan sandan Chadi Paul Manga yace mutane goma sha biyar aka kashe ciki harda mai hari kunar bakin waken.
Kasar Chadi tana taka muhimmiyar rawa a yunkurin da rundunar sojan yankin ke yi na fafatawa da yan kungiyar Boko Haram.
Ta wani gefen kuma da sanyin safiyar yau Asabar wani mai harin kunar bakin wake cikin a daidaita sahu dake gudu kusa da ofishin jami'an tsaro a Maiduguri tayi bindiga ta kashe dukkan fasinjoji hudu dake cikin a daidaita sahun.
Wannan harin na nuni da irin barazanar da yan kungiyar Boko Haram suke jawowa Nigeria, duk da ikirarin da rundunar soja tayi cewa ana samun nasarar yaki da yan Boko Haram
Wani mai harin kunar bakin wake ya kai kari wata kusa birnin Ndjamena kasar Chadi ya kashe mutane goma