Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MAIDUGURI: 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Tayar da Bamabamai


Banabanai sun sake tarwatsewa a Maiduguri
Banabanai sun sake tarwatsewa a Maiduguri

Yayinda mataimakin shugaban kasa Farfasa Osinbajo yake kai ziyara sansani 'yan gudun hijira dake Maiduguri a jihar Borno wasu 'yan kunar bakin wake biyu sun tayar da bamabamai.

Wasu 'yan kunar bakin wake su biyu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun tayar da bamabamai yau Laraba kusa da wani asibiti a Maiduguri babban birnin jihar Bornon Najeriya.

Fashewar bamabaman sun zo ne daidai lokacin da mataimakin shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo yake kai ziyara a sansanonin 'yan gudun hijira wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita.

'Dan kunar bakin waken farko ya tada bam ne a daidai karfe 11.30 na safe kusa da kofar shiga asibiti inda wasu 'yan kunar bakin wake suka taba kashe mutane uku da raunata mutane 16. A wannan karon mutane biyu sun ji ciwo.

Bam na biyu ya faru ne 'yan mintuna biyu bayan tashin na farko. Wannan ya kashe dan kunar bakin waken tare da jikata wasu mutane biyu dake kusa da wurin inji wani Muhammad Haruna wanda ya taimaka wurin daukan wadanda suka jika zuwa samun jinya.

Tun lokacin da Muhammad Buhari ya zama shugaban kasar Afirka da ta fi kowace kasa a nahiyar yawan jama'a da girman tattalin arziki da kuma mayar da Maiduguri hekwatar yaki da ta'adanci, 'yan Boko Haram suka kara zafafa kai hare hare cikin birnin da kewaye.

Babu tabbaci ko an auna hare-haren ne kan asibitin ko kuma bam din ya tarwatse ne kafin a kaishi wurin da kungiyar ta shirya zata kai hari.

Shi asibitin yana daya daga cikin wuraren jama'a dake bayan gari da ake kira Molai wurin da bashi da ingantaccen tsaro kamar cikin tsakiyar Maiduguri.

Farfasa Yemi Osinbajo yana ziyarar sansanonin 'yan gudun hijira ne dake da tazarar kilomita 10 daga inda bamabaman suka tashi. Akwai kimanin 'yan gudun hijira miliyan daya da rabi wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita a cikin shekaru shida da 'yan ta'adan suka kwashe suna fafutikar kafa daular Islama a arewa maso gabashin Najeriya.

XS
SM
MD
LG