Mukaddashin Darektan hulda da jama'a na rundunar mayakan Najeriyan, yace an kashe akalla mayakan Boko Haram su 20 ko fi, wadansu daga cikinsu kuma suka sami raunuka a lokacinda sojoji suka sake kwato Dikwa daga hanun 'yan binidgar wadanda suka sake mamaye wuraren da sojojin kasashe makwabta kamar kamaru suka kama, amma bayan da suka janye, sai 'yan binidgar suka sake mamaye su.
Da yake magana da Ibrahim Alfa Ahmed, kanal Sani Usman yace a fafatawar da suka da 'yan binidgar a wani gari da ake kira Farjari tsakanin Dikwa da Maiduguri, sun kama motoci biyar wadanda aka dana bama-bamai a cikinsu, da babura, da kuma wata mota kirar Toyota wacce aka girke binidga mai sarrafa kanta, wacce zata iya harbo jiragen sama.
Da yake bayanai kan dalilin da yasa aka sauya taken yakin da suke yi da 'yan binidgar, daga "Matakin zaman lafiya" zuwa "zaman lafiya dole",kanal Usman yace ganin an yi amfani da lallashi, da nasiha da kiraye kiraye, wadannan 'yan binidgar basu da wata sha'awa na zaman lafiya. Shine yasa sabon Hafsan hafsoshin Najeriya Manjo Janar Yusuf Burutai, yace yanzu zaman lafiya dole ne, ko 'yan Boko Haram suna so ko basu so, tilas a maido da zaman lafiya.
Ga karin bayani.