Shedun gani da ido sunce yan yakin sa kan kungiyar Boko Haram sun kashe mutane goma sha daya da suke zargi da laifin ficewa daga ciki kungiyar.
Mazauna garin Miringa dake dab da Biu, jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria sunce kafin ketowar alfijirin jiya Juma'a mayakan kungiyar Boko Haram suka kutsa garin suka rika bi gida gida suna neman wadanda suke zargi da laifi ficewa daga cikin kungiyar.
Wani mazaunin Miringa mai suna Mallam Mohammadu Kimba ya fadawa yan jarida ta wayan tarho cewa da gari ya waye ne aka ga gawarwarkin mutane goma sha daya da aka yiwa yanka rago a filin salar idi. Yace dukkan mutane goma sha dayan basu dade da zuwa garin ba, dama kuwa mazauna garin sunyi zaton akwai yiwuwar mutanen yan Boko Haram ne.
Haka ma a jiya Juma'a anji karaji harbe harbe kusa da Maiduguri baban birnin jihar Borno. Shedun gani da ido a kauyen Zabamari sunce jiya Juma'a da dare yan Boko Haram suka kai hari garin, suka fafata da sojojin Nigeria.
An dorawa kungiyar Boko Haram laifin kai hare hare da dama a wannan makon da kuma kashe fiye da mutane dari da hamsin a tarzoma mafi muni tun lokacin da shugaba Muhamadu Buhari ya dare kan ragamar mulki a ranar ashirin da tara ga watan Mayu.
'Yan kungiyar Boko Haram sun yiwa mutane goma sha daya yanka rago a Miringa kusa da Biu jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria