Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaikayi ya koma kan mashekiya ga wani da yayi kokarin kai hari


Wata mota dauke da jama’a tayi kokarin arcewa daga tashe-tashen hankula a birnin Maiduguri.
Wata mota dauke da jama’a tayi kokarin arcewa daga tashe-tashen hankula a birnin Maiduguri.

Wani mai harin kunar bakin wake cikin a daidaita sahu da yayi kokarin kai hari a Maiduguri, kaikayi ya koma kan mashekiya domin bam din ya tashi ya kashe shi.

Da misalin karfe bakwai na safe mazauna birnin Maiduguri suka ji kara mai karfi, wanda daga bisani aka samu labarin cewa tashin wani bam ne da wani mai harin kunar bakin wake yayi yunkurin kaiwa akan wata mota daga fito daga tashar Borno Express.

Wakilin sashen Hausa Haruna Dauda Biu ya aiko da rahoton cewa mai harin kunar bakin wake yayi amfani da a daidaita sahu lokacinda yayi kokarin apkawa motar, amma bai samu nasarar ba.

Bam din ya tashi ya halaka shi mai harin kunar bakin waken. A saboda haka jami'an tsaro suka tsananta binciken aaben hwa, al'amarin daya hadasa cunkoson akan titunan birnin Maiduguri

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG