Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kare Hakkin ‘Yan Jarida Ta Kasa Da Kasa Ta Nuna Damuwa Akan Take Hakkin ‘Yan Jarida A Yankin Sahel


An Gudanar Da Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar
An Gudanar Da Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar

Kungiyar kare hakkin ‘yan jarida ta kasa da kasa Reporters Sans Frontieres wato RSF a takaice ta bayyana damuwa a game da abinda ta kira yanayin tsaka mai wuyar da ‘yan jarida suka shiga a yankin Sahel.

NIAMEY, NIGER - Kungiyar ta RSF ta nuna damuwa ne musamman a kasashen dake karkashin gwamnatocin soja inda hukumomi da kungiyoyin ta’addanci ke barazana ga rayuwar manema labarai.

A rahoton da ta fitar a farkon makon nan ne kungiyar Reporters Sans Frontieres ta ce hukumomi da ‘yan ta’adda a yankin sahel sun hurawa ‘yan jarida wuta inda aka bada labarin abinda ya shafi tashin hankalin da ake fuskanta a yankin na Sahel da ke kara zama wani abu mai matukar wuya ga manema labarai.

Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar
Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar

Hakan ke nufin yankin Sahel na fuskantar barazanar zama wurin da ya fi ko ina toshe hanyoyin samun labarai a baki dayan nahiyar Afirka, a cewar Malan Boubacar Diallo wakilin wannan kungiya a Nijar.

Cibiyar ‘yan jarida ta kasa wato Maison de La Presse a ta bakin sakataren yada labaranta Souleymane Oumarou Brah na cewa ba wata tantama game da bayanan rahoton na RSF. Ya na mai jaddada cewa, babu shakka ‘yan jarida na fama da matsin lamba a yankin Sahel.

Kungiyar ta gargadi gwamnatocin kasashen wannan yanki su sake tunani dangane da mummunar fahimtar da suke yi wa aikin jarida kasancewarsa daya daga cikin gimshikan samar da zaman lafiyar al’umma.

Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar
Shagulgulan Bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida A Nijar

Wannan matsala ta tauye ‘yancin aikin jarida a yankin Sahel, wani abu da ya fi tsananta a kasashen da ke karkashin mulkin soja kuma, inda a ke fama da matsalolin tsaro.

Lamari na baya-baya shine wanda ya wakana a Burkina Faso inda hukumomi suka kori wakilan wasu kafafen kasar Faransa saboda laifin saba ka’idodin aiki.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Kungiyar Kare Hakkin ‘Yan Jarida Ta Kasa Da Kasa Ta Nuna Damuwa Akan Toye Hakkin ‘Yan Jarida A Yankin Sahel .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG