Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KAMARU: An Yanke Wa Tsohon Darektan CRTV Hukumcin Daurin Shekaru 12


Amadou Vamoulké
Amadou Vamoulké

Wata kutun musamman mai shari'anta wadanda ake tuhuma da aikata manyan laifukan almundana , ta yanke wa tsohon darektan tashar talabijin ta CRTV Amadou Vamoulké hukumcin daurin shekaru 12 a gidan yari.

Kotun ta sami tsohon darektan da laifin biyan kanshi kudin hutu da ya kai dala dubu 25 a shekara ta 2005 da 2006, a wata sharia’ar da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar kare hakkin ‘yan jarida su ka nemi a sake dubawa.

An kuma same shi da laifin ba jami’an ma’aikatar kudi da aka tura aiki tashar tukuici.

Wata kutu ta musamman da aka kafa domin shari’anta manyan laifukan almubazaranci ce ta saurari karar.

An kama Vamoulke, dan shekaru 72, wanda ya zama shugaban tashar CRTV a 2005, aka kuma tsare shi a watan Yuli 2016 bisa zargin rub da ciki da fadi da dukiyar talakawa.

An yi ta dage sauraron karar har sau 137 cikin shekaru shida da rabi da ake tsare da shi.

Amadou Vamoulké
Amadou Vamoulké

A hirar ta da kamfanin dillancin labarai na Associated Press, lauyar shi Alice Nkom ta ce, “ya kamata a yi fatali da karar baki daya.”

Ta kara da cewa, " an tauye wa Amadou Vamoulke ‘yancin walwala tun kafin a yanke mashi hukumci. An keta hakkin bil’adama ta fannoni da yawa a wannan shari’ar… duniya baki daya ta shaida cewa, an keta doka a tsare shi da aka yi.”

Lauyar ta kuma bayyana cewa, za su daukaka kara. Tun farko lauyar ta shaidawa kungiyar kare hakkin 'yan jarida CPJ cewa, Vamoulké ya kamu da cutar asma, da ciwon jijiyoyi a lokacin da yake gidan yari, kuma ta ce ta nemi a kai shi wani asibitin da ke wajen kasar Kamaru amma aka yi watsi da bukatar ta su. Ta kuma bayyana cewa, ciwon nasa ya kara tsananta a wannan shekarar .

Hukumcin shekaru 12 a gidan yari ya hada da shekaru da ya yi a tsare.

A shekara ta 2020 kungiyar da ke sa ido kan kulle al’umma ba bisa ka’ida ba ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi kira da a saki Vamoulke, ta bayyana cewa, banda rashin lafiya da yake fama da shi, an keta hakinshi a yadda aka gudanar da shari’ar.

Haka kuma kungiyar kare hakkin 'yan jarida-RSF, ta bayyana shekarar da ta gabata cewa, “ana tuhumar shi a kan laifin da bashi da hujja, kuma ya fuskanci makarkashiyar fannin shari’a.”

Bayan yanke mashi hukumci. kungiyar kare hakkin 'yan jarida ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da hukumcin ta kuma yi kira da a ba shi damar kula da lafiyar shi ba tare da bata lokaci ba.

Ofishin CPJ
Ofishin CPJ

A cikin sanarwar da ke dauke da sa hannun Angela Quintal, jami'ar kula da shirin Afirka ta CPJ a birnin New York, kungiyar ta bayyana cewa, "hukuncin da aka yanke wa dan jaridar Kamaru Amadou Vamoulké a ranar Talata bisa zarginsa da laifin almubazzaranci da dukiyar jama'a babban rashin adalci ne, kuma yana iya zama tamkar hukuncin kisa. Vamoulké yana da shekaru 72 kuma ya riga ya shafe fiye da shekaru shida a tsare ba bisa ka'ida ba. Dole ne masu gabatar da kara su amince da neman daukaka karar da ya yi, bisa la’akari da shekarunsa, rashin lafiyarsa, da kuma cunkoso, da rashin tsafta a gidan yari na Kondengui, a ba shi damar komawa gida bisa beli. ba tare da bata lokaci ba.”

Rahoton kungiyar RSF na shekara ta 2022 kan ‘Yancin Aikin Jarida, ya sa kasar Kamaru a matsayi na 118 daga cikin jerin kasashe 180.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG