Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2023: Hukumar Kula Da Kafafen Yada Labarai Ta Amurka USAGM, Ta Horas Da ‘Yan Jarida Kan Tsare Dokokin Aiki

USAGM
USAGM

Hukumar kula da kafafen labarai na ketare ta Amurka wato USAGM, ta hori wakilan kafafen labaru na Najeriya kan yadda za su tsare dokokin aikin jarida idan sun tashi ba da labarai kan yadda za a gudanar da babban zabe har zuwa bayan sanar da sakamako.

ABUJA, NIGERIA - Wannan ya fito ne a karshen taron horar da wakilan kafafen labarun Najeriya da za su dau rahotannin zaben kan dokokin aiki da hukumar ta Amurka USAGM a takaice ta dauki nauyin shiryawa.

Mr. Mwamoyo Hamza, VOA
Mr. Mwamoyo Hamza, VOA

"Mun san wakilan kafafen labarai da su ka halarci taron su na da kwarewa amma ba laifi idan aka sabunta kwarewar ta su wajen gudanar da aiki mai adalci ga kowa" In ji mataimakin daraktan sashen Afirka na Muryar Amurka Mr. Mwamoyo Hamza da ke cikin malaman da su ka horar da wakilan.

Mr. Hamza ya ce sam 'yan jarida su kaucewa karbar wani ihsani daga wasu 'yan siyasa don hakan keta haddin aikin jarida ne da zai iya hana su ba da sahihan labarai.

ZABEN 2023: Hukumar Kula Da Kafafen Labarai Ta Amurka USAGM, Ta Horas Da ‘Yan Jarida Akan Tsare Dokokin Aiki
ZABEN 2023: Hukumar Kula Da Kafafen Labarai Ta Amurka USAGM, Ta Horas Da ‘Yan Jarida Akan Tsare Dokokin Aiki

Nan take daraktan cibiyar koyon dabarun aikin jarida na gidan talabijin na CHANNELS inda aka gudanar da horarwar Mr. Chukwudi Okoli ya karfafa muhimmancin cewa ba laifi ba ne a rayuwa mutum ya zama ya na da aboki dan siyasa amma in an zo fagen aiki to nesantar 'yan siyasar don samun yin adalci shi ne daidai.

Mr. Chukwudi wanda ya ce in dan jarida ya biyewa alaka da ‘dan siyasa zai iya rasa martabar jajircewarsa ga aiki, ya karfafa tsarin daukar labarai ta hanyar jin ta bakin kowane bangare da kuma tantance gaskiyar labari maimakon gaggawar yada abin da bai inganta ba.

ZABEN 2023: Hukumar Kula Da Kafafen Labarai Ta Amurka USAGM, Ta Horas Da ‘Yan Jarida Akan Tsare Dokokin Aiki
ZABEN 2023: Hukumar Kula Da Kafafen Labarai Ta Amurka USAGM, Ta Horas Da ‘Yan Jarida Akan Tsare Dokokin Aiki

Malam Sani Muhammad, jami'in hukumar USAGM din ne a Najeriya ya bayyana yadda hukumar ta Amurka ta dauki aikin horas da 'yan jarida dabarun aiki da muhimmanci.

Wakilan kafafen labarai daga sassan Najeriya sun halarci horarwar ta tsawon yini 3 da karbar takardar shaida.

ZABEN 2023: Hukumar Kula Da Kafafen Labarai Ta Amurka USAGM, Ta Horas Da ‘Yan Jarida Akan Tsare Dokokin Aiki
ZABEN 2023: Hukumar Kula Da Kafafen Labarai Ta Amurka USAGM, Ta Horas Da ‘Yan Jarida Akan Tsare Dokokin Aiki

Hakika 'yan jarida kan fuskanci barazana a lokacin aikinsu a yayin da su ka tsaya wajen bayyana yadda gaskiyar lamura su ke duk da a na samun baragurbi da kan zaman su kan abokan bangaren marasa gaskiya.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-hikaya:

ZABEN 2023: Hukumar Kula Da Kafafen Yada Labarai Ta Amurka USAGM, Ta Horas Da ‘Yan Jarida Kan Tsare Dokokin Aiki
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG