Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Matasa Ke Daukar Ranar Rediyo Ta Duniya


UN Radio Day
UN Radio Day

Yadda Matasa Ke Ganin Radiyo Duk Da Amfani Da Kafafen Sadarwa Na Zamani Ke Yi Wajen Samun Labarai.

Duk da yadda kafofin yada labarai na rediyo ke samun kalubale daga kafofin sada zamunta na zamani, masana sun bayyana cewa rediyo nada tasiri wajen inganta zaman lafiya da ilimantar da al’umma musamman a nahiyar Afrika.

Al’ummar Hausa na cikin jerin al’ummomin da suka shahara wajen sauraron rediyo domin sanin abubuwan dake wakana a yankunansu da sauran kasashen duniya.

Wannan dabi’a ta sanya manyan kafafen yada labaran manyan kasashen duniya ke amfani da harshen wajen yada labarai tun shekaru aru-aru.

Rahoton jami'an kula da harkokin yada labarai na Hukumar Kula Da Kafafen Yada Labarai na Kasa da Kasa na gwamnatin Amurka, na shekarar 2022, ya nuna cewa kashi 77 na 'yan Najeriya na sauraron rediyo akalla sau daya a sati.

Duk da Kasancewar fannin yada labarai na rediyo na samun barazana da gasa daga fannin hanyoyin sadarwa na zamani wanda wani rahoto ya nuna cewa akwai masu amfani da kafofin sadarwa na zamanin sama da miliyan 40 a Najeriya, rediyo na ci gaba da yin tasiri.

Ko har yanzu matasa a kasar na sauraron Rediyo duk da cewa suna samin labarai ta yanar gizo? Wasu ma'abuta rediyo sun bayyana ra'ayoyinsu.

Baya ga na’urar rediyo mutane na sauraron gidajen rediyo ta hanyar amfani da wayoyinsu har ma a motoci, ko har yanzu rediyo na da tasiri a rayuwar al’umma? Tambayar da na yiwa Bala Muhammad kenan Malami a sashin koyar da aiki jarida dake jami’ar Bayero a jihar kano, wanda ya ce lallai kuwa, duk da kalubalen zamani da ya ke fuskanta.

Kazalika malam Umar Saleh Gwaani kwararre a fannin sadarwa na zamani kana masanin tsaro na hanyoyin sadarwa wato cyber security ya yi bayani makamancin wannan.

Taken Ranar Rediyo ta Duniya ta bana shine Rediyo da Zaman Lafiya, musamman yadda za a yi amfani da rediyo wajen zaman lafiya a cikin al’umma.

Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim daga Abuja, Najeriya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
XS
SM
MD
LG