Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an tsaron Siriya ko Sham sun hallaka mutane 17


Tankokin yakin Sham kenan ke tayar da kura a yayin da kowa ya gudu
Tankokin yakin Sham kenan ke tayar da kura a yayin da kowa ya gudu

‘Yan gwagwarmaya sun ce jami’an tsaron Syria ko Sham sun kashe

‘Yan gwagwarmaya sun ce jami’an tsaron Syria ko Sham sun kashe akalla mutane 17 a jiya Jumma’a, a yayin da mutane sama da 200,000 su ke yin zanga-zangar nuna kyama ga gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.

‘Yan gwamgwarmayar sun ce akarin mace-macen sun auku ne a yankin Homs mai fama da tashin hankali, a inda dinbin mutane su ka taru don bayyana rashin amincewarsu da dage taron gaggawa kan Sham da kungiyar kasashen Larabawa ta yi wanda ada aka aje yau Asabar don yinsa.

Kafafen yada labarai sun ce kungiyar ta dage taron ne don ta bai ma Sham karin lokaci don ta sami sukunin kauce ma takunkumi ta wajen amincewa da tsarin da zai kawo karshen tashe-tashen hankulan.

Gwamnatin Sham ta musanta zargin ‘yangwagwarmayar da cewa babu wani mace-mace ko kuma take hakkin bil adama a jiya Jumma’a. Kafar yada labarai mallakin gwamnati mai suna SANA ta kuma ce an ma yi zanga-zangar goyon bayan gwamnati a yankin yammacin kasar.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG