Kungiyoyin kare hakkin bil adama sunce sojojin kasar Sham (Syria) sun hallaka akalla mutane biyar a yau Alhamis, a daidai lokacinda tawaggar ‘yan kwamitin gani-da-ido na kasashen Larabawa suka warwatsu zuwa yankunan da gwamnati ke kokarin murkushe masu yi yi mata zanga-zangar nuna mata kyama.
Masu hakoron kare hakkokin sunce wasu daga cikin kashe-kashen gillar an yi sune a kusa da Damascus, babban birnin kasar, inda sojan suka bude wuta akan masu jayyaya da gwamnati.
Duk wannan tana faruwa ne yayinda ‘yan kwamitin gani-da-ido na kasashen Larabawan ke harramar zuwa wurare irinsu Daraa, Hama da Idlib don su gani in da gaske gwamnati take, zata daina abkawa masu yi mata zanga-zanga kuma ta saku fursunonin siyasa