Ana nan ana shirin kai dauki a kuduncin Kasar Filifinu, wanda wata mummunar isaka mai ruwa ta addaba, wadda ake jinma ta share daukacin kauyuka zuwa cikin teku.
Mahaukaciyar iska mai ruwa da ake kira Washi, ta farma yankin Mindanao, ta game yankin da ruwa kamar da bakin kwarya da kuma iska mai yawa. Ruwa mai iskan ya kuma hadda munanan ambaliya da gocewar laka.
Jiya Asabar kungiyar Red Cross da ke Filifinu ta yi kiyasin cewa mutane 436 ne su ka mutu, bisa ga yawan gawarwakin da aka kidaya a wuraren shirya gawarwaki. Sakatare Janar na kungiyar Gwen Pang ya gaya ma Associated Press cewa an yi kusa sa’o’i 24 ba tare da wani ya zo daukar wasu daga cikin gawarwakin ba, wanda hakan ke nuna mai yiwuwa daukacin iyalan sun halaka.
Hukumomin Filifino sun ce har yanzu ba a san inda daruruwan mutane su ke ba, a daidai lokacin da masu ayyukan ceto ke zakulo karin gawarwaki daga cikin laka.