Sakataren tsaron Amurka, Leon Panetta, ya ayyana kawo karshen yakin Iraqi a lokacin wani bukin da aka gudanar a babban filin jirgin saman Bagadaza.
A bayan da aka sauko da tutar rundunar sojojin Amurka, aka kuma rera taken sojoji mai suna “Last Post” jiya alhamis, Panetta ya shaidawa sojojin cewa Amurkawa da ‘yan Iraqi masu yawa sun zub da jininsu, amma kuma an cimma gurin wanzar da kasar Iraqi wadda zata iya mulkin kanta.
Sojojin Amurka fiye ad dubu 4 da 500 sun mutu da kuma wasu dubban ‘yan Iraqi a lokacin wannan yakin da sojojin taron dangi suka kaddamar a kasar ta Iraqi har ya kai ga kifar da gwamnatin Saddam Hussein. Sojojin Amurka fiye da dubu 32 sun ji rauni. Haka kuma, Amurka ta kashe kudi akalla dala miliyan sau dubu dari takwas, watau biliyan 800, a wannan yaki na Iraqi.
Ya zuwa jiya alhamis, sojojin Amurka kimanin dubu 4 kawai suka rage a kasar ta Iraqi, daga cikin sojoji har dubu 170 da aka girka a kasar a tsakiyar wannan yaki. Sauran sojojin na Amurka zasu janye daga Iraqi nan da ranar asabar na makon gobe, watau nan da kwana takwas.
Panetta yace wadannan sojoji zasu bar Iraqi da sanin cewa sun taimakawa al’ummar kasar wajen kafa sabon babin da babu mulkin danniya cikinsa a tarihin kasarsu, tare da fatar kwarai ta karuwar arziki da zaman lafiya.
Yace a yanzu Iraqi ta rungumi makomarta, amma kuma Amurka zata ci gaba da zama babbar kawa wadda zata kasance tana da abinda ya kira ma’aikatan diflomasiyya masu gagarumin yawa.