Masu sa ido na kungiyar hadin kan larabawa sun fara ziyara a birnin Homs na kasar Siriya da ake fama da tashin tashina a cikin shirin tabbatar da cewa gwamnati ta cika alkawarinta na janye tankoki da dakarunta daga biranen ta kuma saki fursunonin siyasa.
Kafar watsa labarai ta kasar Siriya tace masu sa idon sun gana da gwamnan Homs yau Talata, kwana daya bayanda ‘yan gwaggwarmayar kare hakin bil’adama suka yi kira ga masu sa idon su ziyarci birnin.
Yan gwaggwarmaya sun ce jami’an tsaron gwamnati sun kashe a kalla mutane 30 a birnin Homs jiya Litinin. Bisa ga cewarsu, dakarun gwamnati sun zafafa kai hare hare a birnin cikin ‘yan kwanakin nan, amma suka janye kafin isowar masu sa idon.
Yan gwaggwarmaya sun ce a kalla masu zanga zanga dubu ishirin suka taru a birnin Homs yau Talata domin wani gangami a daidai lokacin ziyara ta masu sa ido.