Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe mutane 250 a Syria ciki kwanaki biyu


Wannan hoto da aka samu ta hanyar sadarwar internet, masu zanga zangar ne ke dauke da gawar Tameg a Homs.
Wannan hoto da aka samu ta hanyar sadarwar internet, masu zanga zangar ne ke dauke da gawar Tameg a Homs.

Hukumar masu hamaiya ta kasar Syria ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Larabawa da su dauki wani mataki a Syria.

Hukumar masu hamaiya a kasar Syria, ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Larabawa da su dauki wani mataki, bayan rahotani sunce sojojin gwamnatin Syria sun kashe fiye da mutane 200 a cikin kwanaki biyu.

Yau Laraba, wannan hukuma ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta kira wani taron gaggawa domin tattauna karkashe mutane da aka yi a tsanin Zawiyah da Idlib da kuma Homs. Ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana wadannan yankuna a zaman tudun mun tsira, ta tilasta sojojin Syria janyewa daga wadannan wurare.

Kungiyar ko kuma hukumar tace an kashe mutane dari biyu da hamsin cikin kwanaki biyun da suka shige.

Jiya Talaa wata kungiyar kare hakkin jama'a ta fadawa Muryar Amirka cewa sojoji sun yiw fara hula kawanya suka kai musu hari a lardi Idlib da kuma kauyen Kafruwed. Kungiyar tace akwai ma lokacinda jami'an tsaro suka file kan limamin wani Masalaci.

Shedun gani da ido sun fadawa kungiyar kare hakkin Bil Adama cewa sun farma wasu sojoji bijirarru a Idlib, suka kashe ko kuma raunana kimamin dari daga cikinsu. An bada rahoto cewa akwai wasu fara hula da suma aka kashe.

Ba'a dai tabbatar da sahihanci wannan labari daga wata kafa ta fisabillilahi ba, domin gwamnatin Syria tana takurawa yan jaridun kasashen waje.

An bada rahoton kai wannan hari ne a yayinda masu lura na kasa da kasa suke shirin zuwa Syria wani yunkurin kawo karshen tarzomar da aka yi watani tara ana yi a kasar.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG