Talbijin din gwamnatin kasar Kuriya ta arewa ya bada labarin cewa shugaba Kim Jong Il ya mutu bayan shekaru 69 a duniya.
Wata mai karanta labarai a talbijin ta ce ya mutu a ranar Asabar sanadiyar gajiya. Wasu rahotanni sun ce ya mutu ne sanadiyar tsayawar zuciya, kuma a lokacin ya na balaguro a jirgin kasa.
Kim Jong Il ya kama mulki ne a shekarar 1994 bayan mutuwar mahaifin sa Kim Il Sung wanda ya kafa kasar Kuriya ta Arewa. Babu sahihin tarihin rayuwar Mr.Kim mai yawa. Ba kasafai ake ganin shi a bainar jama'a ba, kuma ba a cika saka muryar sa ta kafofin yada labarai ba.
Watakila a fi tuna shi a zama wanda ya bunkasa shirin nukiliyar kasar Kuriya ta Arewa, a yayin da miliyoyin 'yan kasar sa maza da mata ke mutuwa da yunwa.
A karshen shekarar da ta gabata Mr. Kim ya karawa dan autan sa Kim Jong Un matsayi ya ba shi mukamin janar mai taurari hudu, a cikin wani abun da aka fassara da cewa wani yunkuri ne na neman ganin dorewar gadon mulki daga uba zuwa da, a daular Kwaminisancin wadda ita kadai ce irin ta a duk fadin duniya
Masu fashin bakin al'amura sun ce a tsaya a gani ko za a samu jayayyar neman shugabanci tsakanin manyan janar-janar din sojin kasar ko kuma da zai gaji uban sa cikin ruwan sanyi.