Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kurtu Manning Yana Son Alkali Ya Janye


Shugaban Dandalin WikiLeaks a Ingila.
Shugaban Dandalin WikiLeaks a Ingila.

Lauyan da yake kare sojan Amurka da ake zargi da fallasa sirrin Amurka ga dandalin WikiLeaks ya bukaci alkali da yake sauraron shari’ar ya janye.

Lauyan da yake kare sojan Amurka da ake zargi da fallasa sirrin Amurka ga dandalin WikiLeaks ya bukaci alkali da yake sauraron shari’ar ya janye.

A fara sauraron shaida kamin a fara shari’ar gadan gadan, na tuhumar kurtu Bradley Manning, lauyansa David Combs, ya dage cewa alkalin yayi aiki da ma’aikatar shari’a ta Amurka a matsayin mai gabatar da kara, lokcin yana farar hula. Ma’aikatar shari’an tana gudanar da wani bincike daban kan mai dandalin Wikileaks Julian Assange, wadda kurtun Bradley Manning ya gabatarwa bayanan sirrin gwamnatin Amurka.

Wan zaman kotun da aka yi a sansanin soja da ake kira Fort Meade d a bashi da nisa da birninn Washington, ana gudanar da shi ne da nufin tantance ko Manning zai fuskanci sharia a kotun soja.

Ana zargin Manning da satar sirrin gwamnati, wadda daga bisani ya baiwa WikiLeaks. Dandalin WikiLeaks ya fara wallafa bayanan cikin watan Yuli na bara.

Wallafa wadan nan bayanan sirri ya tada kura tsakanin kasashen Duniya, domin sun bayyana abinda Amurka take cewa maras dadi dangane da shugabannin kasashen Duniya.

Haka kuma jumma’an nan, kotun kolin Ingla ta yanke hukuncin mai dandalin WikiLeaks Julian Asange, yana iya daukaka kara a kokarin da hukumomin Sweden suke yin a ganin an mika mata shi domin ya fuskanci zargin laifuffuka da suka shafi harka da kananan ‘yan mata.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG