Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo yayinda yake jawabi a taron tsaro da kwalajin runudunar sojoji na koyas da dabarun yaki ya shirya ya ce babu ko tantama dakarun Najeriya sun karya lagon 'yan Boko Haram.
Sai dai mataimakin ya kira a kara himma akan tattara bayanan sirri domin taimakawa sojoji da wasu jami'an tsaro da bayanan. Ya ce alhaki ne da ya rataya akan sojoji da jami'an tsaro da masu fada a ji a kasar da ma jama'a gaba daya. Injishi hakkin 'yan kasar ne su tabbatar da cewa kasar ta ci gaba da zama daya cikin kwanciyar hankali.
Taron tsaron na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin aika aikar Boko Haram na karuwa a jihohin Yobe da Borno da Adamawa. Kwana kwanan nan 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata 110 a garin Dapchi a jihar Yobe. A garin Madagali kuwa dake jihar Adamawa kodayaushe ne 'yan Boko Haram ke kai harin kunar bakin wake. Haka a garin Rann cikin jihar Borno 'yan Boko Haram din sun kai wani wawan hari inda suka kashe sojoji da wani likita tare da sace ma'aikatan kiwon lafiya uku.
Tsohon gwamnan soja a jihohin Kano da Binuwai Kanar Aminu Isa Kontagora ya ce shi bai yadda a ce soja ya gudu ba. Amma soja na iya ja da baya idan ba zai iya mayar da wuta ba. Injishi sojojin Najeriya sun yaki Boko Haram a koina sun kwato duk wuraren da suka mallaka da can. Ya kira mutane su tashi tsaye su taimakawa sojoji da bayanai ba wai su soma shimfida tabarma ba suna son yin walwala.
A cewar Air Commodore Gamawa dole ne shugaban kasa ya sa ido akan kudaden da ake aikawa sojoji, ya tabbatar sun kai wurinsu. Ya tabbatar ana biyan dakarun dake yaki da 'yan Boko Haram.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum