Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yaye Tsoffin Mayakan Kungiyar Boko Haram Da Suka Samu Horo


Tsoffin mayakan kungiyar Boko Haram da suka mika kansu sun samu horaswa ta tsawon makonni 16 da suka hada da sake masu akida da sarkakesu da kuma horas da su sana'o'i daban daban.

Tsoffin mayakan Boko Haram da aka yaye sun dauki alkawarin zama 'yan kasa na gari yayin da aka yi bikin yaye su..

Tsoffin mayakan da suka mika kai sun samu horaswa na tsawon makonni 16 wadda gwamnatin tarayya ta dauki alhakin shiryawa tare da horasa dasu sana'o'i daban daban.

Kwararru da kuma masana da malaman addinin musulunci suka wa'azantar dasu da tsarkakesu ta hanyar cire masu tsatsauran ra'ayi domin mayar da su garuruwansu na asali.

Daya daga cikin wadanda suka samu horon ya yi jawabi inda ya godewa gwamnatin tarayya akan horon da aka basu da kulawa dasu da horas dasu sana'o'i daban daban domin samun dogaro ga kai yayinda suka koma wurarensu na asali. Ya roki mutanen dake waje da su yi hakuri dasu, su yafe masu abubuwan da suka wuce. Ya yi fatan duk 'yan Boko haram da shugabansu Abubakar Shekau zasu tuba wata rana.

Gwamnan Gombe Alhaji Hassan Ibrahim Dankwambo shi ya yi jawabi a madadin gwamnaonin jihohin arewa maso gabashin kasar. Bayan ya roki al'ummar kasa su karbi wadannan tubabbun, ya ba tsoffin mayakan tabbacin cewa yanzu daidai suke da kowane dan kasa. Injishi babu wanda zai nuna masu wani bambanci.

Daga karshe an mika mutanen ga gwamnonin jihohinsu domin su mayar da su garuruwansu na asali.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG