Hukumar tace ana gudanar da bincike a kan harin. Tace abin da ka agano a yanzu shine, mayakan Boko Haram masu yawa, dauke da makamai da bindigogi masu sarrafa kansu da rokoki da gurneti sun kai hari a kan sojoji.
Mai magana da yawun hukumar kula da bakin hauren ta kasa da kasa Joel Millman, yace, ya san cewa akwai sansanin yan gudun hijira na cikin gida a wurin. Millman yace ma’aikatan hukumar bakin hauren dake aiki a sansanin sun ce an kashe sojoji hudu, da yan sanda hudu da kuma ma’aikatan jinkai uku, yayin da wasu a’aikatan guda uku ke fama da rauni kuma mutum guda a cikinsu ya bata.
Joel Millman yace kwai bayani da na samu daga Mohammed Abdiker, darektan ayyuka da jinkai na hukumar, yana cewar, muna bakin ciki da alhinin na kashe abokan aikinmu guda biyu a cikin wani hari da yan Boko Haram suka kai a Arewa maso gabshin Najeriya da yammacin Alhamis. Yace Ibrahim Lawan da Yawe Emmanuel sun taka rawan gani wurin taimakawa fararen hula da yan gudun hijiran cikin gida. Yace zamu kewarsu.
Facebook Forum