Yayin da ake fadi-tashin gano inda 'yan mata Dapchi aka boye su, wani rahoto ya yi nuni da cewa jami’an sojoji a Najeriya na da masaniyar hare-hare da za’a kai a yankin, duk da cewar ba a ambaci takamaiman wuraren da za a kai harin ba.
Wani rahoto da shafin yanar gizon yada labarai na Sahara Reporters ya fitar, ya nuna cewa za’a kai harin ne a jihohin Borno da Yobe.
Shafin ya ruwaito cewar hakan bai sa jami’an tsaron dauki matakan da suka kamata ba.
A maimakon haka ma sai aka samu janyewar dakarun a yankin Dapchi wanda hakan ya haifar da sace ‘yan-matan makarantar 110.
Rahoton ya nuna cewa an samu bayanai da suka cewa sojoji su yi hankali musamman da motoci kirar Golf, wadanda akan yi amfani da su wajen kai hare-hare a shalkwatar jihohin Borno da Yobe.
Sai dai cewar wani babban jami'in sojin Najeriya, Kanar Oyema Uwachuku, an janye sojojin ne don wata bukata da ake da ita a garin Kanama da ke bakin iyaka da kasar Nijar.
Kuma ya ce an mika ragamar tsaron garin na Dapchi a hannun jami’an ‘yan sanda kafin ficewarsu.
Sai dai rundunar ‘yan sanda ta musanta hakan.
Kwamandan rundunar yaki da Boko Haram ‘Opration Lafiya Dole’ Manjo Gen. Nicolas Rogers, ya ce a koda yaushe a shirye suke don gamawa da kungiyar ta boko haram da kawo zaman lafiya a kasar baki daya.
Ya kara da cewar ba wai suna kokarin daura laifi ne akan wani ba, illa dai a mayar da hankali wajen kawo karshen matsalar.
Wasu daga cikin iyayen yaran da aka sace a makarantar ta Dapchi, sun ce basu da bukatar tone-tone, babban bukatarsu ita ce gwamnati ta maida hankali wajen ganin an kwato musu ‘yayansu cikin gaggawa.
Facebook Forum