Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Najeriya Zasu Kare Makarantun Jihohin Arewa Maso Gabas


Gamayyar Jami'an tsaron Najeriya dake kai ziyara makarantu ta na ba da tabbacin aiwatar da tsaro a makarantu
Gamayyar Jami'an tsaron Najeriya dake kai ziyara makarantu ta na ba da tabbacin aiwatar da tsaro a makarantu

Biyo bayan yadda 'yan Boko Haram suka sace daliban makarantar mata dake Dapchi, shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya umurci jami'an tsaro su tabbatar da tsaro a duk makarantun jihohin arewa maso gabas lamarin da ya sa yanzu suna ziyarar makarantun

Gamayyar jami'an 'yan sandan Najeriya da jami'an kare jama'a da ake kira Civil Defense ta kai ziyara a wasu makarantun jihar Borno, inda ta yi wa daliban alkawarin basu kariya ta musamman.

Jami'an tsaron sun ce irin abun da ya faru a makarantar mata dake Dapchi inda aka sace wasu 'yan mata ba zai sake faruwa ba cikin ikon Allah.

Jami'an tsaron sun hada da babban sifeton 'yan sandan Najeriya, da babban kwamandan Civil Defense, Alhaji Abdullahi Gana, wadanda suka zaga makarantu su na ba daliban kwarin gwuiwa saboda abun da ya faru a Dapchi.

Babban sifeton 'yan sandan wanda mataimakinsa ya wakilta ya yiwa daliban jawabi tare da cewa "mun zo ne domin mu karawa daliban kwarin gwuiwa game da batun tsaronsu saboda abun da ya faru a makarantar mata dake garin Dapchi kuma mun zo ne bisa umurnin shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari don mu tabbatar da cewa mun samar da tsaro a duk makarantun arewa maso gabas"

Ya kara da cewa ba zasu bari irin hakan ya sake faruwa ba inda za'a zo a kwashe dalibai haka kawai. Zasu ba duk makarantun jihohin tsaro.

Shi ma kwamandan Civil Defense Alhaji Abdullahi Gana ya yi karin haske game da ziyarar tasu inda ya ce duk jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Gombe zasu basu tsaro. A cewarsa zasu tsara sunayen jami'an tsaro da zasu tura makarantun amma ya ki ya bayyana yadda zasu yi aikin sabili da dalilan tsaro.

A saurari rahoton Haruna da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG