Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Agajin Likitoci Ta MSF Ta Dakatar Da Ayyukanta A Garin Rann Jihar Borno


A wannan hoton da aka dauka a ranar 29 Yulin 2017, Wata mata ce ke tafiya a cikin sansanin da ke Garin Rann.
A wannan hoton da aka dauka a ranar 29 Yulin 2017, Wata mata ce ke tafiya a cikin sansanin da ke Garin Rann.

Bayan mummunan harin da aka kai garin Rann da ke Jihar Borno a ranar alhamis 1 Maris, kungiyar agajin likitoci ta dakatar da ayyukan da ta ke yi a garin kuma ta kwashe ma’aikatanta na gida da na kasashen waje.

A cewar kungiyar, har yanzu ba a san adadin mutanen da aka kashe da wadanda suka jikkata ba amma sun baiwa mutane 9 kulawa kafin suka bar garin.

Mutane dubu arba’in ne da suka dogara kan kungiyar agajin a garin Rann domin samun kiwon lafiya.

“Kyale marasa lafiya ciki har da yara 60 da ke cin moriyar shirin samar da abinci ba tare da kulawa ba a wannan sansani, wannan al'amari ne mai ban takaici a garemu.” Inji jami'ar tsare-tsaren gaggawa ta kungiyar a Najeriya, Kerri Ann Kelly.

Ta kara da cewa kungiyar za ta sa ido ta jira da zaran yanayi ya inganta za ta dawo ta ci gaba da aiki.

Shugaba Buhari yayi tir da harin da aka kai inda ya bayyana cewa, “Wadannan hare-haren Boko Haram sun karawa gwamnatinmu karfin kudirin kawo karshen ta’addancin kungiyar a cikin kankanin lokaci. Ina jajantawa Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin agaji da ke aiki a garin Rann Jihar Borno."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG