Ma'aikatan agaji uku run rasa rayukansu, inda kuma wata ma'aikaciyar jinya guda daya ta sami rauni.
Mista Edward, ya ce ma'aikatan sun sadaukar da rayuwarsu wajen samar da kulawa ga jama'ar da bala'i ya rutsa da su, musamman ma mata da yara.
Ya kuma yi kira ga mahukunta da su tabbatar da cewa sun bankado wadanda suka aikata harin, su kuma fuskanci shari’a.
Cikin mutanen uku da suka rasa rayukansu, biyu daga ciki jami'ai ne a wani sansanin 'yan gudun hijira a Rann, Sannan na ukun likita ne.
Ya ci gaba da cewa mutane miliyan 7.7 ne suke bukatar taimako a wannan shekara ta 2018 a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.
Edward, ya kuma ce shekaru tara kenan ake fama da tashe-tashen hankula da ya ki ci ya ki cinye wa, wanda ya yi sanadiyar samun 'yan hijira da dama da ke bukatar taimako.
Facebook Forum