A jiya Laraba ne hukumar EFCC din ta gayyato tsohon gwamnan jihar ta Borno Ali Modu Sheriff wanda ya isa ofishin hukumar da misalin karfe goma na safe.
Yan jarida da suka hada da wakilin Muryar Amurka sun ziyarci ofishin hukumar dake Maiduguri amma basu iya shiga harabar ba saboda tsauraran matakan tsaro.
Tsohon gwamnan dai ya bayyana ne a harabar hukumar inda aka umurceshi ya ajiye motarsa a waje kana ya taka da kafa domin shiga harabar.
Bayanai daga ofishin hukumar na nuni da cewa ta ajiye tsohon gwamnan har na tsawon awa biyar tana yi masa tambayoyi kan nera miliyan arba'in da biyar da aka ce ya amsa a hannun karamin ministan, Barrister Wakil wanda shi ma dan asalin jihar Borno ne.
Shi ma karamin ministan a makon da ya gabata hukumar ta EFCC ta gayyaceshi domin amsa tambayoyi dangane da karban wasu kudade da suke da alaka da harkokin zabe.
Sanata Ali Modu Sheriff shi ne tsohon gwamna na farko da hukumar dake Maiduguri ta gayyata kuma shi ne gwamnan da ya bude ofishin lokacin da yake mulki tare da tsohuwar shugabar hukumar EFCC din Farida Waziri.
Jama'ar Maiduguri na cigaba da ganin tsoffin shugabanni na ta kai komo a harabar ofishin, lamarin da ba zai rasa nasaba da tambayoyin da hukumar ta ke yiwa mutanen ba, musamman ma wadanda suka rike mukaman gwamnati.
Ga karin bayani.