Shugaban jamiyar PDP na kasa Sanata Ali Modu Sheriff ya ce bai wakilta wani ya yi magana a madadin sa ba a cigaba da musayan zazzafan kalamai tsakanin bangarorin jam’iyar da ke neman darewa gida biyu wanda ya samo asali daga batutuwan shugabanci da na rabon mukamai gabannin babban taron ta na kasa a Fatakwal ranar Asabar mai zuwa.
Shugaban jam’iyar PDP ya furta haka ne a hirarsu da wakilin Muryar Amurka Sanusi Adamu a filin saukar jiragen sama na Jalingo fadar jihar Taraba kan hanyarsa ta komawa Abuja bayan babban taron jam’iyar shiyyar Arewa maso Gabas . A bayan taron, shiyyar Arewa maso Gabas ta tsaida Sanata Ali Modu Sheriff a matsayin dan takarar ta na shugaban PDP na kasa.
Da yake amsa tambayar matakan da ya ke son dauka kan rigingimun da suka dabaibaye jam’iyar bayan zaben jami’anta a wasu jihohin Najeriya ciki har da Adamawa da jihar Sakkwato, Sanata Sheriff ya ce kawo yanzu ba a sanarda ofishin uwar jam’iyar ko mika mata wasu korafe-korafe ba.
Ga karin bayani.