Ana dai tumarsa ne kan sama da wasu Miliyoyin Naira da maimakon ya sanya kudin kan kafofi na ayyukan da yayiwa wani kwamiti, sai ya karkata kudaden zuwa asusunsa na musammam. Wannan kamu na Mr. Orasanya shine na baya bayan nan akan irin manya manyan jami’ai na sojoji da farar hula da hukumar EFCC ke taso keyarsu a gaba wurin gurfanar da su gaban kuliya.
Daya daga cikin jami’an hulda da jama’a na hukumar EFCC, Mallam Baba Mohammed, yace akwai wani kwamiti da shi Mr. Orasanya ke shugabanta a zamanin gwamnatin da ta wuce, inda ya rubutawa babban bankin Najeriya cewa kwamitinsa yana bukatar tallafi, an kuma bashi kudi kimanin Naira Miliyan 100 sai ya bude wani asusun banki da sunan kwamiti din ya ci gaba da amfani da kudin ta wasu hanyoyi.
Haka kuma akwai kudaden da aka basu daga gwamnati na gudanar da harkokin kwamiti, amma yayi ta yin yadda yake so da su. Haka zalika ya saka kudaden cikin wani sashe na kasuwanci a cikin bankin da yake da asusun, wanda hakan ya sabawa dokar kasa.
A baya dai an kama tsohon shugaban ma’aikatan Mr. Steven Orasanya a shekarar da ta gabata, kan wasu makurden kudade har ma aka gurfanar da shi gaban kotu. Wanda yanzu haka ana ci gaba da wannan shari’ar.
Wannan dai babban kamu ne da hukumar EFCC ta yiwa Mr. Steven Orasanya, wanda yake daya daga cikin masu fada a ji, a kusoshin gwamnatin Najeriya tun zamanin gwamnatin Olushegun Obasanjo har lokacin da Jonathan ya sauka mulki.
Domin karin bayani.