Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sanya Dokar Hana Fita A Karamar Hukumar Mangun Jihar Filato


Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang
Gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang

Gwamnatin jahar Filato ta sanya dokar hana yawo na awoyi ishirin da hudu a karamar hukumar Mangun jihar Filato.

Sanya dokar ta biyo bayan tabarbarewar tsaro ne a cikin garin na Mangu.

A wata sanarwa daga gwamnatin jihar Filato ta ce ta dauki matakin hana zirga-zirga ne bayan tattaunawa da ta yi da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki,

Sanarwar ta kara da ce wa masu gudanar da ayyuka na musamman ne kadai ke da izinin zirga-zirga, har sai yadda hali yayi.

Duk kokarin ji daga hukumomi da al'ummar da wakiliyar Muryar Amurka ta kira da aikewa sakonni, ya ci tura.

To sai dai wadansu da basu amince a nadi muryarsu ba sun shaida min cewa da safiyar yau Talata lamarin yayi kamari, inda har an kona gidaje da masallaci a cikin garin na Mangu.

A halin da ake ciki dai rikicin na sassan jihar Filato, na ci gaba da sanadin rasa rayuka da dukuyoyi.

A taron manema labarai da Hadaddiyar Kungiyoyin Fulani suka kira a Jos, sun bayyana yadda ake kisan dauki dai-dai wa al'ummarsu.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar Filato, Nura Muhammad Abdullahi yace al'ummarsu ta sha fama matuka a rikice-rikicen dake faruwa.

Suma a nasu martani, Kungiyoyin Al'ummomin Jihar Filato, karkashin jagorancin Barista Dalyop Solomon Mwantiri, yace sun gano cewa an gayyato mutane ne da suka hallaka mutane fiye da dari biyu a karshen watan jiya.

Gwamnatin jihar Filato dai tayi alkawarin daukan matakai don kawo karshen hare-hare da rikice-rikice a tsakanin al'ummar jihar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG