A wani yanayi na nuna bacin rai, wasu fusatattun mutane, galibin su mata, sun kona gidan Hakimin garin Bokkos, Monday Adanchi.
Mutanen yankin da su ka fusata na zargin Adanchi da yin watsi da su a cikin mawuyacin lokaci da ake fama da kashe-kashen mutane a wasu sassan karamar hukumar ta Bokkos da ke jihar Filato.
Rahotanni sun nuna cewa, kona gidan basaraken ya biyo bayan kisan gillar da aka yi a jajibirin Kirsimeti da ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 160.
Zanga-zangar dai ta faru ne da sanyin safiyar ranar Juma'a 5 ga watan Janairu, 2024.
Matan da su ka gudanar da zanga-zangar sun bayyana kokensu, kan yadda aka tsare wasu matasa, biyo bayan gano gawar wani mutum a wata unguwa a garin na Bokkos.
Matan da suka yi zanga-zangar sun zarce zuwa gidan Hakimin, bayan sun lura da rashin zuwansa ofishin 'yan sandan, sai suka yi ta jifa, inda daga bisani suka kona gidansa tare da kone motoci biyu.
Jami'an tsaro sun yi gaggawar kwantar da tarzomar don hanata yin kamari a tsakanin al'umma.
Matan sun kuma nuna rashin jin dadi kan yadda hukumomi ke tafiyar da al’amuran tsaro da kuma yadda hukumomin kananan hukumomi da na tarayya su ke yin sakaci da batun tsaro a yankin.
Izuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomi ba su ce kome kan batun ba.
Dandalin Mu Tattauna