Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Allah-Wadai Tare Da Kira A Bincike Hare-Haren Da Aka Kai Jihar Filato


Babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Volker Türk
Babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Volker Türk

Babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya bayyana matukar damuwarsa a kan wasu hare-hare da aka kai a kauyukan jihar Filato da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 200, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar.

Hare-haren sun faru ne tsakanin yammacin ranar Asabar zuwa safiyar Talatan ranar bikin Kirsimeti.

Babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya fitar da sanarwar a shafin hukumar na X (twitter) inda ya bukaci mahukuntan Najeriya da su gaggauta gudanar da bincike kan lamarin, bisa ga dokokin kare hakkin bil'adama na duniya. Ya kuma jaddada mahimmancin hukunta dukkan wadan da aka same su da hannu cikin kai harin.

"Ya kamata gwamnati ta kuma dauki matakai masu ma'ana don magance musabbabin da ke haifar da hakan da kuma tabbatar da rashin sake afkuwar wannan mummunan tashin hankali," in ji Turk.

A yankunan arewa maso yammacin Najeriya da tsakiyar Najeriya, ‘yan bindiga sun dade suna tayar da tarzoma, suna kai hare-hare daga sansanonin dazuzzuka, suna kwasar dukiyoyi na haram, da kuma yin garkuwa da jama’a domin neman kudin fansa.

Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Kashim Shettima Ya Kai Ziyarar Jaje Jihar Filato
Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Kashim Shettima Ya Kai Ziyarar Jaje Jihar Filato

Akwai kuma rikici mai tsanani tsakanin makiyaya da manoma musamman d sakamakon karuwar yawan jama'a biyo bayan matsi na yanayi da ya kara ta'azzara tashe-tashen hankula a cikin al'umma, wanda ke kara haifar da tashin hankali.

Yankin jihar Filato yanki ne da ya dade yana fama da rikicin addini da na kabilanci na tsawon shekaru da dama.

Yankin arewa maso gabashin Najeriya dai na fama da rikicin jihadi tun shekara ta 2009, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da raba mutane kusan miliyan biyu da muhallansu.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ke kan karagar mulki tun watan Mayu, ya jaddada kudirinsa na tabbatar da tsaro tare da Allah wadai da irin wadannan munanan hare-hare da ‘yan ta’adda ke kaiwa al’umma wadanda basuji ba kuma basu gani ba.

Lokacin Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Kashim Shettima Ya Kai Ziyarar Jaje Jihar Filato
Lokacin Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Kashim Shettima Ya Kai Ziyarar Jaje Jihar Filato

A wata sanarwar manema labarai da ya fitar daga fadar shugaban kasa, Cif Ajuri Ngelale, mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ya bayyana cewa, Shugaba Bola Tinubu yayi Allah wadai da hare-haren baya bayan nan a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar Filato, inda aka yi asarar rayuka sama da 115 a daren ranar 24 ga watan Disamba. neman yankin da abin ya shafa.

Haka zalika, Shugaban yayi alkawarin tabbatar da bincike da zakulo wadanda ke da hanu cikin harin tare da hukunta su.

Lokacin Da Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Kashim Shettima Ya Kai Ziyarar Jaje Jihar Filato
Lokacin Da Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Kashim Shettima Ya Kai Ziyarar Jaje Jihar Filato

A nashi bangaren, gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya tabbatar da mutuwar mutane da dama, ya kuma bayyana hare-haren a matsayin “hare-hare na rashin Imani”, yana mai jaddada mummunar illar da harin ya haifar ga al'ummomin dake shirye-shiryen bukukuwan Kirsimeti cikin lumana a lokacin.

~Yusuf A. Yusuf~

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG