Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Hankali Na Baya Baya Nan A Jihar Filato Ya Jefa Mazauna Sansanin 'Yan Gudun Hijira Cikin Halin Matsi


Bayan tashin hankalin da ya auku a karshen makon 2023, daruruwan 'yan gudun hijira dake sansanoni da dama, a ciki da wajen jihar Filato, sun bukaci agajin gaggawa daga hukumomi da daidaikun jama'a.
Bayan tashin hankalin da ya auku a karshen makon 2023, daruruwan 'yan gudun hijira dake sansanoni da dama, a ciki da wajen jihar Filato, sun bukaci agajin gaggawa daga hukumomi da daidaikun jama'a.

'Yan gudun hijiran daga bangaren Fulani da sauran kabilun yankunan Kananan Hukumomin Mangu, Bokkos da Barkin Ladi a jahar Filato, sun tsinci kansu a sansanonin biyo bayan hare-haren da ya auku a yankunan nasu, wanda yayi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi da kona gidajensu.

A wurin wani taron manema labarai da hadaddiyar kungiyoyin Fulani suka kira a cikin garin na Jos, sun koka kan yadda suka shiga halin tashin hankali ba tare da an kula su ba.

'Yan gudun hijira da ke neman agaji
'Yan gudun hijira da ke neman agaji

Imam Abubakar Isah Ahmad daga garin Bokkos, yace tun a baya da matar Shugaban Kasa ta kawo tallafi, rabon bai kai kansu ba.

yace al'ummarsu, tayi asara da yawa.

Ita kuma Madam Mary Isah dake gudun hijira a cikin garin Bokkos, ta ce suna bukatar abinci, abin kwanciya, tufafi da sauran kayayyaki na bukatun rayuwa na yau da kullum.

Shugaban Kungiyar Miyetti Allah a jihar Filato, Alhaji Muhammad Nura Abdullahi
Shugaban Kungiyar Miyetti Allah a jihar Filato, Alhaji Muhammad Nura Abdullahi

Da ya ke bayani, Pastor Iliya Joshua Tat, wanda shima ya ke gudun hijira, yace alkaluman mutane dake gudun hijira a inda yake sun kai dubu goma sha biyar.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta Tsakiya kuma Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, yace nan gaba kadan zasu shirya taro na masu ruwa da tsaki don magance matsalolin tsaro a yankin.

a saurari rahoton Zainab Babaji:

Mazauna sansanonin 'yan gudun hijira na cikin gida sun bukaci a tallafia musu.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG