Shugaban gwamnonin na jihohin tsakiyar Najeriya ya jaddada cewa ba rikici ne na manoma da makiyaya ba, amma batagarine ke sintirin kashe al'umma da basu yi musu laifin komai ba.
Yace “yaya zamu magance shi, saboda ba zamu bar lamarin yana faruwa loto-loto ba. Dalilin zuwanmu kenan mu fada maka cewa, kaine zaka dauki mataki na tattaro dukkan masu ruwa da tsaki ba tare da al'akari da inda suke ko su wanene ba''.
Gwmana Abdullahi Sule ya bukaci yin amfani da na'urori na fasaha don ganowa da kamo batagari da hukuntasu.
Gwamnan jahar Binuwai, Rabaran Fada, Hycinth Alia, wanda yace shima jaharsa na fuskantar matsalar tsaro, yace ba zasu zuba ido suna kallon 'yan ta'adda na kisan mutane ba.
Rabaran Alia yace ''hadin kai muke bukata a Arewa ta tsakiya don zaman lafiya''.
Shi kuwa gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, yace shima jaharsa na fama da matsalar tsaro ya kuma jaddada muhimmancin tattaunawa musamman da 'yan ta'adda.
''Yana da muhimmanci mu duba hanyoyin warware matsaloli ba tare da amfani da karfi ba. Ba rikicin makiyaya da manoma bane, ta'addanci ne, kuma ba'a tattaunawa da 'yan ta'adda" in ji shi.
A martaninsa, gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang yace shiyyar Arewa ta tsakiya tana da dimbin arziki don haka dole ne su nemi hanyoyin kare al'umma don samun ci gaba.
“Ya kamata mu farfado da mitin na gwamnonin Arewa ta tsakiya don hadin kai da tunani kan magance matsalolin da suka addabe mu,'' a cewar gwamnan na jihar Filato
Kungiyar gwamnonin jihohin tsakiyar Najeriyan sun kuma bada tallafin naira miliyan dari, don sake tsugunar da wadanda rikicin ya shafe su a kananan hukumomin Bokkos da Mangu.
A halin da ake ciki kuma, hukumar lafiya ta duniya ta tallafawa jahar Filato da kayakkyakin asibiti don kulawa da wadanda suka sami raunuka suke kwance a asibitoci ake musu jinya.
Kyayyakin sun hada da bandeji, plasta, bakin allura, auduga, safan hannu da sauransu, sun kai na miliyoyin daloli.
Ga rahoton Zainab Babaji daga Jos din Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna