Fafaroma ya roki Allah ya kubutar da Najeriya daga bala’in da ake yi na hallaka rayuka da 'yan bindiga ke yi ba kakkautawa.
Sama da mutane 160 ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kashe a kauyuka da dama na kananan hukumomin Mangu, Barkin Ladi da Bokkos na jihar, a daidai lokacin da duniya ke bukukuwan kirsimati, lamarin da ya tada hankalin duniya.
Bayan isar da sakonsa na Angelus na yau da kullun a ranar Lahadi, Paparoma ya mayar da hankalinsa ga tashe-tashen hankula na baya-bayan nan.
“Abin takaici, bikin Kirsimati a Najeriya ya fuskanci munanan tashe-tashen hankula a jihar Filato, inda aka kashe mutane da dama.
"Ina yi musu addu'a da iyalansu. Allah ya kubutar da Nijeriya daga wannan ta’asa!” a cewar fafaroma.
A wani mataki na nuna damuwarsa kan abubuwan dake faruwa a duniya, Fafaroma Francis ya kuma tuna da wasu da ke fuskantar matsaloli a sauran sassan duniya, ciki har da wadanda suka mutu sakamakon fashewar wata motar tanka a Laberiya da kuma wadanda suka fada cikin mawuyacin hali na yaki a Ukraine, Falasdinu, Isra'ila, Sudan, da Rohingya, da dai sauransu.
“A ƙarshen shekara, bari mu tambayi kanmu: Mutane nawa ne rikicin makami ya daidaita? Nawa ne suka mutu? Kuma nawa ne suka halaka, ke cikin wahala, da talauci?”.
Fafaroman ya bukaci masu ruwa da tsaki a yankunan da rikice-rikicen ke aukuwa da su yi biyayya ga lamirinsu, kuma su yi la'akari da irin wahalar da mutane ke ciki.
Kafin jawabinsa mai ratsa jiki kan tashin hankalin na baya-bayan nan, Fafaroma Francis ya yi magana game da inganta rayuwar iyali, inda ya kwatanta gwagwarmayar dangin Yesu Kiristi a duniya, da kuma yadda wassu ke fuskantar rikici a yau.
Dandalin Mu Tattauna