PLATEAU, NIGERIA - Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a wata ziyarar jaje, ga wadanda suka hadu da ibtila'in hare-haren 'yan bindiga a garin Bokkos, da ke jihar Filato.
Mataimakin shugaban kasar wanda ya bayyana takaicinsa kan kisan mutane fiye da dari, da lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira, ya ce gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don taimaka wa wadanda bala'in ya shafa.
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang wanda shi ma ya nanata yunkurin gwamnatinsa na tabbatar da cewa wadanda suka aikata mugun aikin sun fuskanci hukunci, ya kuma ce zuwan mataimakin shugaban kasar ya nuna cewa gwamnati na da niyyar taimakawa.
Hakimin Gundumar, Mbar a karamar hukumar Bokkos, Danjuma Rafan ya ce harin ya basu mamaki saboda babu wani abin da ya hada su da abokan zamansu.
Shi kuma shugaban kungiyar Fulani ta Gan Allah a karamar hukumar Bokkos, Saleh Yusuf Adam ya ce su ma a bangarensu an sa ce musu dabbobi an kuma kashe musu mutane.
Tun farko shugaban karamar hukumar Bokkos, Monday Kassa ya ba da adadin mutane dari da arba'in da takwas ne aka kashe a kauyuka ishirin da biyar.
Gidaje dubu daya da dari biyu da casa'in aka kona kurmus.
Maharan sun kuma kona motoci tamanin da daya, babura dari da tamanin da bakwai, injinan ban ruwa dari biyu da sittin da bakwai, yayin da mutane tamanin da takwas da suka sami munanan raunuka suke kwance a asibitoci suna jinya.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:
Dandalin Mu Tattauna