Rundunar 'yan sanda a jahar Filato tace mutane 79 ne 'yan bindiga suka hallaka a kauyuka goma sha biyu a karamar hukumar Bokkos da wassu 17 a karamar hukumar Barkin Ladi.
A wata sanarwa da kakakin 'yan sandan jahar filato, DSP Alfred Alabo ya aikewa manema labarai a yau Talata, ta nuna cewa 'yan bindigar da har yanzu ba'a sansu ba, sun kona gidaje 221, sun kuma kona babura 27 da motoci guda takwas.
Hare-Haren wanda aka fara tun ranar Asabar zuwa Litinin, ya sanya dubban mutane, musamman mata da yara, da suka tsira da ransu, yin gudun hijira a manyan garuruwa.
Mr Isaac Julson, kansila mai wakiltar Butura a karamar hukumar Bokkos, yankin da kashe-kashen ya fi yawa, yace maharan sun fado wa mutane cikin dare ne suka hallaka su.
Malam Saleh Yusuf Adam, shugaban kungiyar fulani ta Gan Allah a karamar hukumar Bokkos yace wassu al'ummomin yankin sun kona musu gidaje fiye da goma sha biyar.
Wani dan asalin karamar hukumar ta Bokkos, Danjuma Mabas yace tun shekara ta dubu biyu da goma sha takwas da aka yi rikici a kauyukan, aka karkashe mutane ciki har da sarakuna, lamarin ke ci gaba da aukuwa.
Yakubu Ibrahim Iroh, Daraktan kungiyar dake fafutukar zaman lafiya da samarwa Fulani 'yanci yace sai an yi zaman tattaunawa na gaskiya don warware matsalolin dake tsakanin makiyaya da manoma, shine kadai zai samadda waraka.
Ko a farkon wannan shekara, irin wannan salon kashe-kashe yayi sanadin rasa rayukan jama'a fiye da dari a karamar hukumar Mangu, wanda har yanzu al'ummumomi da dama ke gudun hijira a ciki da makwabtan jihohin jahar Filato.
A jiya Litinin, 25 ga watan Disamba, kamfanin dillancin labarai ta AFP ta ruwaito cewa akalla mutane 160 ne‘yan bindigan suka kashe a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna