Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Sojan Amurka Da Laifin Kashe Fararen Hular Afghanistan


Zanen Saje Calvin Gibbs, a zaune, da lauyansa Phil Stackhouse tsaye a tsakiyar kotu lokacin shari'arsa a sansanin soja na Lewis-McChord a Jihar Washington
Zanen Saje Calvin Gibbs, a zaune, da lauyansa Phil Stackhouse tsaye a tsakiyar kotu lokacin shari'arsa a sansanin soja na Lewis-McChord a Jihar Washington

Masu gabatar da kara sun ce Saje Calvin Gibbs ya jagoranci gungun sojoji biyar 'yan ina-da-kisa wadanda suka kashe fararen hula haka siddan

Wata kotun sojoji ta samu wani sojan Amurka da laifin kashe fararen hula ‘yan Afghanistan da ba su dauke da wani makami haka siddan.

Jiya alhamis aka samu Saje Calvin Gibbs, mai shekaru 26 da haihuwa, da wannan laifin, kuma zai fuskanci hukumcin daurin rai da rai.

Masu gabatar da kara suka ce Gibbs ya jagoranci wani gungun sojoji biyar ‘yan ina-da-kisa. Laifuffukan da aka tuhume shi da aikatawa sun hada da kisan kai da kuma sare yatsun mutanen da suka kashe domin ajiyewa a zaman abin ado.

An same shi da aikata dukkan laifuffukan da aka tuhume shi cewa ya aikata din.

Wadanda sojan ya kashe sun hada har da wani saurayi dan shekaru 15 wanda suka samu a wani fili suka harbe shi, sannan suka dauki hoto da gawarsa.

Gibbs ya ki amsa laifinsa, amma uku daga cikin gungun ‘yan ina-da-kisan sun amsa laifuffukansu, aka kuma yi musu sassauci wajen yanke hukumci. Biyu daga cikinsu sun bayarda shaida a lokacin shari’arsa a wani sansanin sojan dake Jihar Washington a yammacin wannan kasa. Soja na biyar yana jiran shari’a.

Ana daukar laifuffukan da suka aikata a cikin ayyukan rashin imani mafiya muni da aka taba gani a shekaru 10 da aka yi ana yakin Afghanistan.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG