Manyan jigogin majalisar mulkin wucingadi na Libya (NTC) sunce mayakansu dake neman cafke garin Sirte sun kashe tsohon shugaban kasar Moammar Gadhafi a garin haihuwar tashi, Sirte din.
Jami’an na NTC sun fada yau a birnin Tripoli cewa mayakansu sun kashe Gadhafi din kuma ma suna rike da gawarsa. Koda yake akwai karancin bayanai gameda yadda al’amarin ya faru, an nuna hotunan gawar wani mutum da yayi kama sosai da Gadhafi din a gidajen telebijin da dama na duniya.
Nan bada jimawa ba ake sa ran shugaban majalisar NTC din, Mustafa Abdel Jalil zai yiwa al’ummar Libya jawabi. Ita ma rundunar NATO bata tabattar da mutuwar Gadhafi ba amma dai tace jiragenta sun saki bama-bammai akan wasu motoci biyu na magoya bayan gadhafi da aka ga suna shawagi a cikin Sirte a yau Alhamis. Ance mayakan NTC dake Sirte sunyi ta harbe-harbe cikin iska da yin tsallen murna yayinda suke daga sabuwar tutar kasar a yau.
A halin yanzu dai shugabannin kasashen duniya na ta kokarin tabattarda gasjkiyar kashe shugaban na Libya. A nan Washington, jami’an fadar White House da na Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka duk suna ta kai gwauro da mari don tabattarda gaskiyar wannan labarin.
Sakatariyar ma'aikatar harkokin Wajen Amurka Hilary Clinton, wacce yanzu haka take ranagadin Afghanistan, tace mutuwar Gadhafi zata zama albishir da zai sawwaka al’amurran Libya, koda yake tace mutuwarsa ba zata sa a zo karshen rikicin da ake fama da shi a Libya ba.
Su ma shugabannin kungiyar kasashen Turai biyu, Herman Van Rompuy da Jose Manual Barrosso duk sun ce mutuwar Gadhafi tasa anzo karshen mulkin mallaka a Libya