Umar Faruk Abdulmuttalab, dan Nigerian nan da ake zargi da laifin kokarin tarwatsa wani jirgin saman fasinjan Amirka da wani bam daya boye a kampensa ya amsa dukkan laifuffukan da aka caje shi da aikatawa.
Idan dai har aka same shi da laifi, to ana iya yanke masa hukuncin dauri rai da rai dangane da wannan danyen aikin da yayi niyar aikatawa a ranar Kirisimetin shekara ta dubu biyu da tara.
Yau Laraba Umar Faruk ya amsa dukkan laifuffuka guda takwas da ake zarginsa da aikatawa, ciki harda aikata ta’adanci da kokarin yin kisa da kokarin amfani da mugun makami.
Umar Faruk yace, ta hanyar bada gudumawarsa ga jihadi akan Amirka, yana sauke nauyin ko kuma alhakin daya rataya a wuyansa a zamansa na Musulmi wanda ke daukan fansa ko kuma yin ramuwar gaiyar kashe Musulmin da basu san hawa ba basu san sauka ba a kasashen Yamal da Afghanistan da kuma wasu wurare da Amirka take yi.
Idan dai ba’a mance ba, fasinjoji da ma’aikatan jirgi ne suka fi karfinsa a lokacinda bam din dake cikin kamfensa yaki ya tashi a lokacinda jirgin saman daya ke ciki, wanda ya taso daga Amsterdam zuwa Detroit ke da niyar sauka. Maimakon bam din daya boye cikin kamfensa ya tashi, sai ya kama ci.
A watan janairu idan Allah ya kaimu za’a yanke masa hukunci.