‘Yan rajin kare hakkin dan adam sun ce dakarun Syria sun kashe akalla mutane 20 a yayin da ake zanga-zangar kyamar manufofin gwamnati a fadin kasar, a daidai lokacin da gwamnatin ke fuskantar sabbin zarge-zargen cewa ta aikata laifin “take hakkin dan adam.”
Kungiyar Kula da hakkin dan adam a Syria ta ce akasarin mace-macen na jiya Jumma’a sun auku ne a yankin Homs. Jami’an tsaro sun kaddamar da jerin samame a birnin da zummar kamo ‘yan tawaye, ‘yan rajin kare hakkin dan adam din su ka kuma ce an hallaka wasu sojojin Syria a wani al’amari mai kama da kwantan bauna.
Ba a iya tabbatar da adadin wadanda aka ce sun mutu din ba saboda gwamnatin Syria ta hana ‘yan jaridan kasashen waje gudanar da harkoki a kasar.
Wannan tashin hankalin ya zo daidai da bayyana wani rahoton da Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Right Watch ta yi jiya Jumma’a, mai nuna cewa da alamar gwamnatin Syria ta aikata laifukan cin zarafin bil’adama ta wajen kuntatawa da kuma kashe kashe ba bisa ka’ida ba.
Kungiyoyin rajin kare hakkin dan adam da shugabannin ‘yan adawa sun yi kira ga masu zanga-zangar da su bukaci a dakatar da Syria daga kungiyar kasashen Larabawa. Wannan kungiya mai kasashe 22 za ta yi taron gaggawa a yau dinnan a birnin Al-Khahira don tattauna tashin hankalin na Syria.
Taron da za a yi ya biyo bayan saba wa sharuddan yarjajjeniyar da Kungiyar kasashen Larabawan ta cimma waddata ta bukaci Syria ta daina amfani da munanan hanyoyin murkushe masu zanga-zanga.