Jakadu a Majalisar Dinkin Duniya sun gaza cimma daidaito kan bukatar da yankin Falasdinu ya gabatar na neman zama cikakkiyar member majalisar.
Wani kwamitin majalisar mai amincewa da sabbin kasashe ya gana yau jumma’a na wani dan gajeren lokaci domin ya amince da rahoton cewa an sami cijewa. Kafofin yada labarai sun sami kofin daftarin rahoton a farkon makon nan.
Kwmaitin ya fara tantance bukatar cikin watan satumba, bayan da shugaba Mahmoud Abbas na yankin ya gabatarwa majalisar dinkin Duniya yunkurin yankin na zama kasa mai cin gashin kai.
Amma bisa dukkan alamu yankin Falasdinu ya gaza samun kuri’u tara da ake bukata daga cikin wakilai 15 dake kwamitin sulhun.